Kofin Europa -An hada Liverpool da Zenit

gasar europa
Image caption Gasar Europa, an fitar da jadawalin karawar kungyoyi 32.

An fitar da tsarin yadda karawar kungiyoyin kwallon kafa 32 za ta kasance a gasar Kofin Europa, inda Liverpool za ta hadu da kungiyar Zenit St Petersburg ta kasar Rasha a karawar da za a yi ta zagayen farko.

Kungiyar Newcastle kuma za ta fafata da Metalist Kharkiv ta Ukraine yayin da Chelsea za ta hadu da Sparta Prague ta kasar Czech ita kuwa Tottenham za ta raba gari ne da Lyon ta Faransa.

Atletico Madrid ta Spain wadda ke rike da kofin za ta hadu da Rubin Kazan ta Rasha.

Ajax wadda ta sami nasarar shiga gasar a matsayin ta uku daga gasar Zakarun Turai a gaban Manchester City za ta kara da Steaua Bucharest.

A ranar Alhamis 14 ga watan Fabrairu na sabuwar shekara za a yi wasannin farko tsakanin kungiyoyin jerin 32, sannan kuma bayan mako daya a yi zagaye na biyu, inda za a yi tankade da reraya a fidda kungiyoyi 16, wadan da su kuma za su yi karawar zagayen farko ranar 7 ga watan Maris, bayan sati daya a yi zagaye na biyu ranar 14 ga watan Maris.

Karin bayani