Wilshere da wasu sun sabunta kwantiragi

jack wilshere
Image caption Jack Wilshere, ya sabunta kwantiraginsa da Arsenal

Jack Wilshere da Kieran Gibbs da Aaron Ramsey da Alex-Oxlade Chamberlain da kuma Carl Jenkinson sun kulla dogon kwantiragi da Arsenal.

Wilshere dan shekara 20 wanda ya dawo wasa a watan oktoba bayan watanni 15 da ya yi yana jiyya ya sanya hannu a sabon kwantiragi da kungiyar har zuwa shekara ta 2018.

Sauran 'yan wasan kuma sun sabunta kwantiraginsu da Arsenal din na tsawon tsakanin shekaru hudu da biyar.

Akan sabunta kwantiragin nasu kocin Arsenal din Arsene Wenger, ya ce idan ka na da manyan 'yan wasa 'yan Burtaniya ya fi sauki ka iya hada kansu.

Yace ''muna murnar dukkanin wadan nan matasan 'yan wasa biyar sun kulla sabon dogon kwantiragi da mu.

Wenger yana kuma da fatan Theo Walcott shi ma zai amince ya cigaba da zama a klub din.

Kwantiragin Walcott din da Arsenal zata kare a watan Yuni na 2013, kuma kungiyoyin Chelsea da Liverpool da Manchester United da City na harin sa.