Rasha ta soki Amurka bisa bata suna

Vladimir Putin
Image caption Vladimir Putin

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya soki wata sabuwar dokar Amurka wadda ta bata sunayen wasu jami'an Rashan da ake zargi da take hakkin bil adama.

A jawabinsa na shekara shekara, Mr Putin ya ce dokar na bata dangantakarsu kuma ya ce zasu mai da martani.

Ya ce dokar hana Amurkawa daukar yaran Rasha mai sosa rai ce amma kuma ita ce wadda ta dace.

Ko da yake Mr Putin bai ce zai sa hannu kan dokar ba idan har ta samu amincewa ta karshe a majalisar dokokin Rashan ranar juma'a.

Karin bayani