Ma'aikatan Najeriya na shirin shiga yajin aiki

Image caption Wasu shugabanin kwadago na jahar Kano

Shugabannin kungiyoyin kwadago na kasa a Najeriya na gudanar da wani taro a babban birnin kasar Abuja ranar Alhamis, domin tattaunawa kan batun shiga yajin aiki na gama-gari a duk fadin kasar.

'Yan kwadagon sun yi barazanar shiga yajin aikin ne a farkon makonnan domin nuna goyon baya ga ma'aikatan kananan hukumomi na Jihar Filato wadanda ke fito-na-fito da gwamnatin jahar wadda taki biyansu albashin fiye da watanni shida.

Sakataren kungiyar Kwadago ta kasa, NLC, Chris Uyot, ya shaida wa manema labarai cewa a taron ne za su yanke shawara kan batun shiga yajin aikin na kasa baki daya.

Yanzu dai babban abin da a ke takaddama a kai tsakanin gwamnatin da ma'aikatan kananan hukumomin jihar shi ne kin biyan kudaden albashi na watannin da suka shafe suna yajin aiki kan kin biyan su sabon tsarin albashi.

Karin bayani