An garzaya da Mubarak asibiti

Image caption Tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak lokacin ya gurfana a gaban kotu a Alkahira.

Jami'ai a Masar sun ce an dauki tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak zuwa wani asibitin soji, bayan da ya fadi a bandakin gidan kaso ya kuma ji rauni a kansa da kirjinsa a makon da ya gabata.

Kamfanin dillacin labarai na gwamnatin kasar ya ruwaito cewa an dauke Mubarak daga asibitin gidan kason ne domin a dauki hoton kwakwalwarsa.

An dai yankewa Mubarak dan shekaru 85 hukuncin daurin rai da rai ne, dangane da kisan masu zanga-zanga a lokacin juyin juya halin da ya hambarar da gwamnatinsa a shekarar da ta gabata.

Tun bayan yanke masa hukuncin, an sha ba da rahotannin cewa rashin lafiyar Mista Mubarak ya tasananta, amma da dama daga rahotannin ba gaskiya ba ne.

Karin bayani