Kungiyoyi sun yi gargadi a kan tura dakaru Mali

malai
Image caption 'Yan tawaye ne keda iko a arewacin Mali

Hukumomin bada agaji a Mali sun yi gargadin cewa kai harin soji domin kwace arewacin kasar daga hannun masu kaifin kishin Islama da 'yan tawaye na kungiyar 'yan aware zai yi mummunar illa ga jama'a.

A cewarsu hakan zai jawo karuwar rasa matsugunnan jama'a a kasar.

Wasu kungiyoyin bada agaji 10 sun nemi kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi duk abin da za iya domin kare fararen hula idan har sojoji suka shiga kasar.

Kwamitin tsaron na shirin kada kuri'a kan wani kudiri na tura dakarun sojin Afurka rewacin Malin.

Wakilin BBC ya ce kungiyar raya tattalin arzukin kasashen yammacin Afurka, wato ECOWAS ta ce tana da sama da sojoji dubu uku dake cikin shiri kwata kwana.