Ghana ta yi asarar fiye da $7m

Jirgin Argentina a Ghana
Image caption Jirgin Argentina a Ghana

Gwamnatin Ghana tace ta tafka asarar sama da dalar Amurka miliyan bakwai sakamakon tsare jirgin ruwan yakin nan na Argentina da wata kotu dake birnin Accra ta yanke hukuncin yi.

Wani gungun kampanoni wato NML Capital ne dai ya shigar da kara a gaban kotun inda ya bukaci kotun da ta tsare jirgin ruwan yaki har sai gwamnatin Argentina ta biya bashin dalar Amurka fiye da miliyan dari uku da yake bin ta.

Ala tilas ne dai gwamnatin Ghana ta saki jirgin ruwan yakin sakamakon hukuncin da wata kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya ta yanke cewa ta sake shi.

Karin bayani