An sace wani Bafaranshe a Katsina

Wasu 'yan sandan Najeriya
Image caption Matsalar tsaro na cigaba da zama kalubale ga 'yan sandan Najeriya

'Yan sanda a jihar Katsina dake arewacin Najeriya sun tabbatar da sace wani Bafaranshe, Francis Colump a garin Rimi.

Maharan dake dauke da makamai sun kuma kashe wasu 'yan Najeriya biyu, yayin da kuma wani dansandan dake tsaron lafiyar Bafaranshen ya samu rauni daga harbin bindigar maharan.

Kwamishinan 'yan sandan Katsina, Abdullahi Magaji yace an garzaya da dansanda asibiti a jihar Kano domin duba lafiyarsa.

Mista Colump injiniya ne dake aikin a kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar iska a jihar ta Katsina.

'Yan bindigan da ba san ko su wanene ba sun kai harin ne a daren jiya Laraba.

Haka kuma maharan sun jefa wani abin fashewa a caji ofis din 'yan sandan garin na Rimi.