'Ghana ta ciri tuta a fagen demokuradiyya'

Ghana
Image caption Ana yiwa zaben kallon zakaran gwajin dafi ga kasar ta Ghana

Abinda ya fi jan hanakalin mutane a duniya yanzu dai shi ne batun tattalin arziki da inganta tsarin demokuradiyya.

Kuma a duka wannan fanni ana ganin kasar Ghana ta ciri tuta a Afrika.

Kasar dai ta samu yabo ne kan yadda ta shirya zabuka a baya, musamman zaben da ya gabata na shekara ta 2008.

Shugaban kasar John Mahama, mai shekaru 54, na fuskantar babban kalubale daga Nana Akufo-Addo, mai shekaru 68.

Da kuri'a 30,000 aka lashe zaben a zagaye na biyu.

An yaba wa Mr Akufo-Addo na jam'iyyar New Patriotic Party (NPP), kan yadda ya karbi sakamakon zaben kaye, duk kuwa da cewa shi ya lashe zagaye na farko na zaben.

Mr Mahama na jam'iyyar National Democratic Congress, ya hau kan karagar mulki ne bayan da shugaba Atta Mills ya mutu ba zato ba tsammani a watan Yuli.

Ziyarar shugaba Obama

Sabanin kasashen Afrika da dama, akwai zaman lafiya a kasar, kuma tattalin arzikinta na bunkasa, ga kuma karancin cin hanci da rashawa.

Ghana ta shirya zabukan demokuradiyya guda biyu ba tare da matsala ba tun bayan kawo karshen mulkin soji a 1992. Mun shirya tsaf, kuma komai ya kammala, dukkan kayan zabe sun isa mazabu da sauran yankunan zaben

Irin wannan fice da kasar ta yi a fannin demokuradiyya da zaman lafiya, ya sa ta samu yabo daga bangarori daban-daban.

Ita ce kasa ta farko da shugaban Amurka Barack Obama ya ziyarta a nahiyar Afrika tun bayan hawansa kan karagar mulki - inda ya ba yyana kyawun tsarin demokuradiyya a matsayin dalilin da ya kai shi kasar.

Sai dai gabanin zaben na bana, an samu 'yan tashe-tashen hankula, abinda kuma ya sa ake nuna shakku kan abinda ka iya biyo bayan zaben.

'Mun shirya tsaf'

Shugaban hukumar zaben kasar Kwadwo Afari-Gyan, ya shaida wa BBC cewa sun shirya tsaf domin gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan Majalisu.

'Mun shirya tsaf, kuma komai ya kammala, dukkan kayan zabe sun isa mazabu da sauran yankunan zaben', a cewarsa.

Kimanin mutane miliyan 14 ne suka yi rijista domin kada kuri'a a mazabu 26,000.

Akwai dai 'yan takarar shugaban kasa takwas, da kuma daruruwan 'yan takarar kujerun majalisar dokoki 275.

Idan babu wanda ya samu nasara a zaben na ranar Juma'a, za a gudanar da zagaye na biyu ne a ranar 28 ga watan Disamba, idan babu dan takarar da ya samu kashi 50% cikin dari a zagayen farko.

Karin bayani