Obama ya nemi takaita mallakar bindigogi

Shugaba Barack Obama na Amurka
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaba Obama ya kaddamar da wani kwamiti da zai duba yiwuwar rage irin kashe-kashen da ake yi da bindiga a Amurka.

Ya yi na'am da irin bukatar da aka nuna a kasar na hana mallakar makamai bayan da wani dan bindiga yayi kisan kiyashi a wata makarantar furamare a jihar connecticut a makon daya gabata.

Mataimakin shugaban kasar, Joe Biden ne zai jagoranci wani kwamiti da Obama zai kafa wanda zai duba dokoki yaduwar makamai.

Mista Obama ya ce Amurkawa da dama suna goyon bayan tsaurara dokokin mallakar makamai a kasar, kuma dole ne majalisa ta ji kukansu.

Ya ce "'yan Amurka da dama na goyon bayan hana siyarda manyan bindigogin soji , kuma wasu da dama na goyon bayan hana sayar da alburusai da dama."

Shugaba Obama dai ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi nazari a kan dokar domin abun da al'ummar Amurka ke bukata kenan.

Karin bayani