Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Haɗuran mota a Nijeriya

Hadarin mota a Najeriya
Image caption Hadarin mota a Najeriya

A Najeriya galibin manyan hanyoyin zirga- zirga a ƙasar, na cikin wani mummunan yanayi, inda wasu daga cikin hanyoyi ake kiransu tarkon mutuwa saboda tsananin lalacewar da suka yi.

Ganin yadda dubban rayuka da dukiyoyi ke salwanta sanadiyyar rashin kyawon hanyoyi, ya sa a cikin wannan makon majalisar wakilan Najeriya ta gudanar da taron jin ba'asi don gano yadda matsalar take da kuma yadda za'a shawo kanta.

Rahotanni dai sun ambato, shugaban hukumar kiyaye hadura ta Najeriya wato FRSC , Mista Osita Chidoka na cewar a bara mutane fiye da dubu biyu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon haɗarin mota a ƙasar.