BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Najeriya za ta rage lantarkin da take samar wa Nijar da Togo da Benin
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 6 ga watan Mayu, 2024.
Abubuwan da suka kamata ku sani kan zaɓen shugaban ƙasar Chadi na 2024
A ranar 6 ga watan Mayun 2024 ne al'ummar Chadi za su fita rumfunan zaɓe domin zaɓar sabon shugaban ƙasar.
Dalilanmu na maka gwamnonin Najeriya a kotu - SERAP
SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan yadda aka kashe basusukan da gwamnonin suka karɓo
Bidiyo, Anam da Amar: Ma'auratan da ke burin gyara zaman aure ta hanyar TikTok
Burhanat Musa Usman da Yusuf Adamu wasu matasan ma'aurata ne a arewacin Najeriya waɗanda aka fi sani da Anam da Amar a shafukan sada zumunta. Sun yi fice wajen kwaikwayon abubuwan da ke faruwa a tsakanin ma'aurata, kuma ɗaya daga cikin burinsu shi ne su yi tasiri wajen inganta zaman aure.
Waɗanne takunkumai aka sanya wa Rasha, Shin suna aiki kuwa?
Sabbin matakan an ɗauke su ne bayan mutuwar jagorar adawar ƙasar, Alexei Navalny wanda ya rasu a lokacin da yake tsare.
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno
Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran nahiyoyin duniya na 05/05/2024
Fargaba da addu'o'i a birnin Sudan da ke cikin mamaya
Mummunan yaƙin basasar Sudan ya samo asali ne kusan shekara guda da ta gabata, bayan da wasu manyan sojojin ƙasar biyu da suka yi juyin mulki suka raba gari.
Ambaliya ta kashe mutum 60 a Brazil
Hukumomi sun umarci mutanen yankin su gaggauta ficewa
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Rana, 13:59, 6 Mayu 2024, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 6 Mayu 2024, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 6 Mayu 2024, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 5 Mayu 2024, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Waiwaye: Ƙarin albashi da kisan da sanƙarau ta yi wa mutum 85 a Yobe
Wannan maƙala ce da ke duba muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata
'Jami'armu na cin gajiyar kashe-kashen da ake yi a Gaza'
Tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoban bara, ɗalibai a Amurka suka riƙa gudanar da zanga-zanga, ta ƙin fita da yajin cin abinci, da kuma kafa tantuna don zanga-zangar baya-bayan nan.
Ba mu yarda a bai wa Amurka da Faransa damar kafa sansani a Najeriya ba - 'Yan Arewa
Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran nahiyoyin duniya
Mece ce illa da kuma alfanun ƙarin albashi ga ma'aikata?
Yayin da ma'aikatan Najeriya ke jiran ƙarin albashi, masana na cewa ba ƙarin albashi kawai ya kamata gwamnati ta saka a gaba ba, hasali ma da an ɗauki wasu matakai ba sai an kai ga ƙarin ba.
Yadda Iran ke samun tallafin China wajen kewaye takunkuman Amurka
Yanzu dai abin tambaya shi ne ta yaya aka yi Iran ta samu damar kewaye takunkuman da aka ƙaƙaba mata?
Watakila Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza
Kawo yanzu Hamas na nazari kan martani da za ta mayar ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza da aka yi wa kwaskwarima
Matar baturen Binance ta buƙaci Najeriya ta sakar mata miji
Matar da Gambaryan ta ce ta shiga wani mawuyacin hali tun bayan tsare maigidan nata.
Abubuwan da suka kamata ku sani kan guguwar da za ta afka wa Tanzania
Guguwar Hidaya ta fara tunkarowa ne a ranar Laraba a kudancin Tekun Indiya zuwa gabashin Tanzaniya da arewa maso yammacin Tsibirin Comoro.
Bambancin mafi ƙarancin albashi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka
Ƙungiyar ƙwadago na neman gwamnatin Najeriya ta mayar da mafi ƙarancin albashi N615,000 daga N30,000 da yake a yanzu, kuma ta ba ta wa'adin ranar 29 ga watan Mayu.
Ana zargin Isra'ila da laifukan yaƙi bayan kisan yaro Bafalasɗine
Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai alamun take doka a kisan da aka yi wa yaron ɗan shekara takwas bayan duba shaidun da aka tattara.
'Rashin albashi ya sanya mun cire yaranmu daga makaranta'
Wasu ma'aikatan jihar Zamfara fiye da dari sun koka kan yadda aka ki mayar da su bakin aiki, bayan da suka jingine ayyukansu, suka rike wasu mukaman siyasa a lokacin gwamnatin jihar da ta gabata.
Labaran Bidiyo
Wasanni
Saudiyya na farautar Jesus da Partey daga Arsenal, Man Utd na shirin cefanar da Sancho
Arsenal na shirin karban tayi kan sayar da ɗan wasan gaba daga Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 27, a wannan kaka.
Da kyar idan Maguire zai buga wasan FA Cup da Man City
Harry Maguire na fatan zai murmure ya buga wa Manchester United wasan karshe a FA Cup, bayan da ya ji rauni a wajen atisaye.
Liverpool ta dauki fansa a kan Tottenham a Premier
Liverpool ta yi nasarar doke Tottenham da cin 4-2 a wasan mako na 36 a Premier League da suka kara a Anfield ranar Lahadi.
Chelsea ta hau kan Man United bayan ta ragargaji West Ham
Chelsea ta hau kan Manchester United a teburin Premier League, bayan da ta caskara West Ham 5-0 a Stamford Bridge.
Brighton ta kawo karshen rashin nasara shida bayan cin Villa
Brighton ta kawo karshen rashin nasara shida, bayan da ta doke Aston Villa 1-0 a wasan mako na 36 a Premier League da suka kara ranar Lahadi.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.
Nishadi
Shirye-shirye na Musamman
Murya, Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 05/05/24Tsawon lokaci, 11,46
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu tare da Haruna Tangaza
Murya, Amsoshin Takardunku 04/05/24Tsawon lokaci, 12,34
Amsoshin Takardunku tare da Ibrahim Yusuf Muhammad
Murya, Lafiya Zinariya kan tsaftar mataTsawon lokaci, 14,21
Lafiya Zinariya kan tsaftar mata, tare da Habiba Adamu
Murya, Gane Mini Hanya 04/05/24Tsawon lokaci, 13,21
Hukumar kula da ilimin almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ta ce a cikin ƴan watanni za a fara ganin ƙoƙarinta na raba miliyoyin yaran ƙasar da jahilci don taimaka musu cimma burinsu na rayuwa idan sun girma.